Rundunar ‘yan sandan Jihar Katsina ta bayyana cewa ta samu nasarar kwato bindigu 109 wadanda ake harbo jiragen sama daga hannun ‘yan bindiga a Jihar a bayanan da su ka tattara na karshen shekarar 2021.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Jihar SP Gambo Isa shi ne ya sanar da hakan a lokacin da ya ke tattauna wa da kamfanin dillancin Labaran Najeriya NAN.
SP Gambo Isa ya ce bayan kwato bindigun sun samu nasarar kwato wasu manyan makamai daga hannun su Tare kubutar da mutane da shanu da jakuna daga wurin su.

Ya kara da cewa sun kuma yi nasarar kama mutane 999 masu aikata manyan laifuka a Jihar.

Yace daga cikin wadanda su ke zargi da aikata laifuka akwai masu yin fashi da makami da garkuwa da mutane da kuma satar shanu.
Sannan rundunar ta gabatar da mutane 145 a gaban kotu domin girbar abinda su ka shuka kuma su na cigaba da binciken sauran kafin su gabatar da su a gaban kotu.
Haka kuma yan sandan sun cafke mutanen da ake zargi da satar shanu su 244 kuma sun gurfanar da 230 a gaban kotu kafin su gama bincike a kan sauran.
Kuma a shekarar da ta gabata ta 2021 ne dai aka kashe wasu da ake kyautata za ton ‘yan bindiga ne su 38 inda ‘yan sanda biyar su ka rasa rayukan su.
Rundunar sun samu nasarar kama mutane 246 da su ke safarar mutane tare da ceto mutane 63 daga hannun su.