Gwamnatin jihar Kano ta ce za ta ci gaba da shirya addu’o’i na shekara-shekara domin neman zaman lafiya a jihar da ma ƙasa baki ɗaya.

Babban sakataren yaɗa labaran gwamnan Kano Malam Abba Anwar ya bayyana a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai cewar, an shirya taron addu’ar ne domin neman zaman lafiya a kan ta’addancin da ya addabi Najeriya.

Gwamnan jihar Abdullahi Umar Ganduje ne ya bayyana haka a yayin da ya jagoranci mabiya ɗariƙar Tijjaniyya na duniya don yin addu’ar neman zaman lafiya a Najeriya wanda aka gudanar a Kano.

Gwamnatin za ta ƙulla wata alaƙa mai ƙarfi da shugabannin Tijjaniyya na duniya domin neman addu’o’i daga mabiya ɗariƙar domin samun zaman lafiya.

Gwamna Ganduje ya ce za a dinga tura ɗalibai ƙasar Aljeriya domin neman ilimin addinin musulunci.

Gwamnan ya karɓi baƙoncin shugaban ɗariƙar Tijjaniyya na duniya Sheik Sharif Ali Ibn Arabi, jika ga Sheik Ahmad Tijjani.

An gabatar da taron addu’ar a yau Asabar a filin taro na Sani Abacha da ke unguwar Ƙofar Mata a Kano.

Mutane daban-daban ne su ka halarci taron addu’ar ciki har da mabiya ɗarikar ƙadiriyya.

Taron ya samu halartar mataimakin gwamnan Kano da sakataren gwamnatin Kano da ma sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ƙaramin ministan noma a Najeriya ya wakilci shugaban ƙasa a yayin taron addu’ar da aka yi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: