Sojoji a jihar Kaduna sun daƙile wani hari da yan bindiga su ka yi yunƙurin kai wa a garin Kwanan Bataro da ke ƙaramar hukumar Giwa ta jihar.

Kwamishinan al’amuran staro a jihar Samuel Aruwan ne ya sanar da haka a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai.
Ya ce sojojin sun hallaka yan bindiga biyar dagha cikin wadanda su ka yi yunƙurin kai harin.

Sojojin sun samu nasarar dakile harin bayan isa wajen da su ka yi a kan lokaci bayan sun samu bayanai a kan harin yan bindigan.

Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El’rufa’i ya nuna jin daɗins a a bisa nasarar da sojojin su ka samu na daƙile harin.
Yan bindigan na kai hare-hare da dama a jihar Kaduna kuma ƙaramar hukumar Giwa na daga cikin ƙananan hukumomin da ƴan bindiga su ka matsa da kai hare-hare.