A sakamakon rashin matuƙa adaidaita sahu a jihar Kano, motocin gida da na dakon kaya da babura masu ƙafa biyu na ɗaukar fasinja don biya musu buƙatunsu.

Masu tuƙa babur mai ƙafa uku wanda aka fi sani da Adaidaita Sahu sun shiga yajin aiki ganin yadda gwamnatin jihar ke karɓar harajin da su ka ce ya musu yawa.
Hukumar Karota a jihar Kano na karɓar naira dubu takwas domin sabunta lambar ababen hawa masu ƙafa uku, al’amarin da ya ja masu tuƙa adaidaita sahu su ka tsunduma yajin aiki.

Tun daga ranar Litinin ɗin da ta gabata masu babura masu ƙafa biyu su ka fara ɗaukar fasinja har ma da motocin dakon kaya da motocin gida waɗanda ba na haya ba.

Matuƙa adaidaita sahu sun buƙaci a cire musu harajin da aka ce za su sabunta a kowacce shekara tun da gwamnatin na karɓar naira ɗari a wajen su a kullum.