Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ɗage takunkunmin da aka sanyawa dandalin Tuwita bayan cika sharuɗan da gwamnati ta gindaya.

Hakan na ƙunshe cikin watasanarwa mai sanye da sa hannun shugaban hukumar NITDA bayan sahalewa daga ministan sadarwa Isah Ali Pantami.
Shafin Tuwita zai dawo aiki daga ƙarfe 12:00am na daren yau wayewar Alhamis.

An rufe shafin tuwita a Najeriya bayan gwamnatin ƙasar ta yi zargin shafin na taimaka wa wajen haifar da fitina a ƙasar.
