Kakakin rundunar Edward Gabkwet ne ya sanar da haka a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai.
Ya ce rundunar ta kuɓutar da mutane 26 waɗanda aka sace a babbar hanyar Birnin Gwari ta Kaduna.

Ya ƙara da cewa nasarar ta zo ne yayin da jami’an ke gudanar da wani sintiri ranar Laraba.

Daga cikin mutanen da sojojin su ka kuɓutar akwai mata da ƙananan yara.

Matafiyan sun bayyana cewar akwai wasu da aka kashe kuma daga cikin su har da direban mota.

Wani direba ya bayyana cewar an kuɓutar da mutanen ne yayin da sojoji ke mukasayar wuta da ƴan bindigan.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: