Ɗumbin Tarihin garin ne ya sa aka wallafa littafi a kan sa.

Garin Zawaciki na ƙarƙashin ƙaramar hukumar Kumbotso a Kano, kuma Kwamared Abubakar Yahuza Yakubu ya wallafa littafin tarihin garin.

Kwamared Abubakar ya bayyana cewar ɗumbin tarihin da ke cikin garin ne ya sa ya wallafa littafin tarihin garin.

A bayanin sa, ya ce wallafa littafin da ya yi zai taimaka wa ƴan baya musamman ɗalibai domin sanin asalin tarihin garin.

Daga cikin tarihin garin akwai wani lokaci da aka taɓa yin gobara sai da gidajen garin su ka ƙone gaba ɗaya.

Taron ƙaddamar da littafin tarihin garin ya samu halartar manyan shuganni a garin Zawaciki da malamai da sauran su.

Mai garin Zawaciki Abdulƙadir Mu’azzam ya nuna farin cikinsa a dangane da littafin tarihin garin da aka wallafa.

An gudanar da taron ne a ranar Asabar ɗin da ta gabata.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: