![](https://matashiya.com/wp-content/uploads/2020/12/mn-1.jpg)
Aƙalla mutane biyar ne su ka mutu yayin da aka ƙone gidaje da dama a sakamakon rikici tsakanin manoma da makiyaya a jihar Ogun.
Al’amarin ya faru a ƙaramar hukumar Imeko-Afon wanda aka ƙone kayan amfanin da ababen hawa.
![](https://matashiya.com/wp-content/uploads/2021/10/DSC_9894-scaled.jpg)
Rikicin ya fara ne tun a ranar Laraba yayin da aka fara a ƙauyen Idofa lamarin da ya yi sanadiyyar rasa miliyoyin dukiya.
![](https://matashiya.com/wp-content/uploads/2020/02/matashiya-photo-2.jpg)
An ci gab da rikicin har zuwa ranar Alhamis yayin da wani ɓangare su ka mayar da martani domin ɗaukar fansa a kan abin da ya faru.
Tuni aka aike da isassun jami’an ƴan sanda yankin da al’amarin ya faru domin kawo ƙarshen rikicin.
Kwamishinan ƴan sandan jihar Aminbola Onyeyemi ya ce sun gayyaci mahukuntan kowanne ɓangare domin kawo ƙarshen rikicin.
Abimbola ya sanar da haka ne yau Asabar sai dai ya ce ba su kama kowa a sakamakon rikicin ba.