Wasu ƴan bindiga da su ka sace mutane a jihar Neja sun bukaci a ba su jarkar man fetur lita 50 da lemon roba a madadin kudin fansa.
Ƴan bindigan sun kai hari ƙauyukan Kulho, Jigawa, Dogo Fadama, Farin Shinge duka a ƙaramar hukumar Mashegu a jihar Neja.
An kai harin ne tun a yammacin Juma’a sannan su ka kai har ranar Asabar a cikin kayukan a nan ne su ka kashe mutane uku.
Bayan kashe mutane uku a ƙauyukan su ka tafi da sauran mutane 28 wanda daga bisani su ka buƙaci a basu madarar Viju da lita 50 na man fetur da kuma wasu lemon roga a madadin kuɗin fansa.
Ƴan bindigan sun kashe mutane biyu tare da sace wasu mutane huɗu a ƙauyukan Jigawa da Dogo Fadama.
Yayin da su ka sace mutane takwas a ƙauyen Farin-Shinge, sai kuma ƙauyen Kulho da aka kashe mutum guda tare da sace wasu mutane 16.
Haka kuma sun sace baburan mutanen ƙauyukan tare da wasu kayan amfani.
Rundunar yan sanan jihar ba ta ce komai a kan lamarin ba, sai dai mataimakin shugaban karamar hukumar Kontogora ya tabbatar da faruwar lamarinw anda ya ce ƴan bindgidan sun je ne daga Tegina.