Rundunar yan sandan jihar Nassarawa ta yi nasarar kama wani mai suna Ɗan’asabe Edo bisa zargin yi wa wata tsohuwa mai shekaru 80 fyaɗe.
An kama Ɗan’asabe mai shekaru 43 a duniya kuma ɗan asalin jihar Kaduna bisa zargin yi wa wata mata fyade a cikin gidan ta.
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar yan sandan jihar ASP Ramhan Nansel ne ya bayyana nasarar kama mutumin a ranar Lahai.
Ya ce an kama mutumin ne bayanmutanen ƙauyen Garaku sun kai korafi wajen ƴan sana kuma nan take aka kama mutumin da ake zargi.
Bayan kama shi, wanda ake zargin ya ce laifin shaiɗan ne ya sa ya aikata hakan.
Tuni kwamishinan ƴan sandan jihar ya bayar da umarnin mayar da ƙorafin zuwa ashen binciken masu aikata laifuka doin faɗada bincike.
Kasancewar matar da abin ya faru da ita na zaune ne ita kaɗai a gidan hahakn ya sa rundunar ta shawarci al’umma da su inga bai wa tsofaffi kula wa ta musamman don gudun sake faruwar hakan a nan gaba.