Rundunar ƴan sandan jihar Filato ta kama wani mai garkuwa da mutane da ya hallaka kawunsa bayan an ƙi biyan kuɗin fansa.

An yi holen matashin mai shekaru 20 a duniya da wasu sauran masu aikata laifi a helkwatan yan sanda ta jihar a ranar Alhamis.
Matashin da ake zargin sa ya tabbatar da cewar shi ya sace kawun nasa sannan ya kashe shi bayan ya sha giya sai dai ya ce ya na dana sanin abin da ya aikata.

Ya ƙara da cewa su biyar su ka aikata garkuwar sannan su ka nemi kuɗin fansa daga yan uwan wanda su ka sace bayan an ƙi biyan kuɗin ne su ka kashe shi.

Ya ce wannan ne karo na farko da ya akata garkuwa da mutane kuma ya na dana sani a kan abin a ya aikata.
Ƴan sanda sun kama matashin mai suna Sulaiman Ibrahim kuma ana ci gaba da gudanar da bincike a kan sa.