Gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari ya ce Najeriya na bukatar gogagen shugaba wanda zai fitar da ita daga halin da ta ke ciki.

Masari ya bayyana haka ne yayin da ya tarbi Bola Ahmed Tinubu wanda ya ziyarci jihar domin jajanta wa a bisa mutuwar kwamishinan kimiyya da fasaha na jihar.
Gwamnan ya ce a halin da Najeriya ta ke ciki a yanzu akwai bukatar ta samu shugaba wanda ya goge kuma zai mayar da hankali domin fitar da ita daga halin da ta ke ciki.

Ya ce babbar matsalar da ƙasar ke ciki a yanzu shi ne matsalar tsaro, kuma hakan ƙalubale ne babba wanda ya ke bukatar ɗaukin gaggawa.

Ya ƙara da cewa idan da har an inganta harkar ilimi a Najeriya shekaru 50 da su ka gabata da Najeriya ba za ta tsinci kanta a halin da ta ke cki ba a yanzu.
A ɓangaren tsaron jihar, gwamna Masari ya ce gwamnatin jihar ta ɗauki tsauraran matakai illa ƙananan hukumomin Batsari da Faskari ne kaɗai su ke fuskantar kananan matsalolin tsaro