Ministan harkokin cikin gida a Najeriya Ra’uf Aregbesola ya bayyana cewa yawan kai hare hare da ake gidajen gyaran hali kamar kaiwa Najeriya baki daya hari ne.

Ministan ya bayyana hakan ne a ranar Litinin, inda ya umarci dukkan jami’an tsaro da ke kula da gidajen yari da su hallaka dukkan wanda ya ke shirin kaiwa gidajen yari hari.
Umarnin na zuwa ne a lokacin da ministan ya ziyarci gidan gyaran halin da ke Ibadan babban birnin Jihar Oyo.

Kuma ya yi kira ga jami,an tsaron da su kara tsaurara matakan tsaron domin kawo karshe masu yunkurin fasa gidajen yari.
Ya bayyana cewa yin hakan ne kadai zai kawo karshe dukkan masu yunkurin shirya kai hare hare gidajen yarin.

Sannan ya ce wasu mutanen su na gani kamar gwamnati ta gaza wajen kula da gidajen yarin wanda ya musnata hakan.