Gwamnan Jihar Yobe mai Malali Buni ya bayyana cewa Jam’iyyar APC mai mulkin kasa za ta gudanar da babban gangamin zaben ta a ranar 26 ga watan Fabrairu 2022.

Buni ya bayyana hakan ne a taron mata na jam’iyyar APC da ya gudana a yau Talata a babban birnin tarayya Abuja.
Gwamnan ya bayyana cewa jam’iyyar APC ta na dogara da goyon bayan mata inda kuma ta ke cigaba da samun nasara.

Mai malali Buni ya ce akalla a yanzu su na da mambobi miliyan 40 wadanda su ke goyan bayan su.

Ya kara da ce a baya an samu cece kuce a cikin Jam’iyyar APC lokacin da aka tsayar da ranar da jam’iyyar za ta fara gangamin taron ta shekarar 2022.