Daga Amina Tahir Muhammad

Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Abuja, ta ɗage ci gaba da shari’ar da ake yi wa shugaban masu fafutukar kafa ƙasar Biafra, Nnamdi Kanu zuwa gobeLaraba.
Ɗage zaman ya biyo bayan ƙorafe-ƙorafen Kanu na cewa gwamnatin tarayya ta gaza gabatar wa da kotu sabbin tuhume-tuhume 15 da ake masa.

Kanu, ta bakin tawagar lauyoyin da ke karkashin jagorancin Babban Lauyan Najeriya, Cif Mike Ozekhome, ya kara da zargin gwamnatin tarayya da hana shi dama domin kare tuhumar da ake masa.

Ozekhome ya shaida wa kotun cewa an kammala tuhume-tuhumen da aka yi masu ne sa’o’i 24 kacal kafin a fara sauraron karar.
A gobe kotun za ta ci gaba da sauraron ƙarar dominɗaukar mataki ta gaba.