Daga Amina Tahir Muhammad
Da sanyin safiyar Talata ne sojoji da ‘yan bindiga suka yi kazamin artabu a Unguwar Musa Tudun Wada Kudansa da ke Maraban Rido a karamar hukumar Chikun ta jihar Kaduna.
Bangarorin biyu sun samu hasarar rayuka a arangamar da ta haifar da tashin hankali a cikin al’ummar.
Wani shugaban a yankin, Joseph Sauri Garba, wanda ya tabbatar wa Daily Trust faruwar lamarin, ya ce an shafe sa’o’i uku ana gwabza fada tsakanin ‘yan bindigan da sojoji.
Daily trust ta ruwaito cewa ‘yan bindigar sun mamaye al’umma da tsakar dare, da nufin yin garkuwa da mutane.
Kimanin mutane 10 da aka yi garkuwa da su aka ce sojojin sun ceto su.
Rundunar ’Yan sandan jihar ba ta ce komai ba a kan lamarin
‘Yan bindiga sun kai hare-hare daban-daban a Kaduna.