Hukumar Kididdiga ta kasa NBS ta bayyana cewa a watan Disamban shekarar 2021 da ya gabata kayan Abinci sun yi tashin gwauron zabi a Najeriya.

Shugaban hukumar shi ne ya bayyana hakan a lokacin taron manema Labarai da ya gudana a ranar Litinin a babban birnin tarayya Abuja.

Shugaban ya bayyana kayayyakin da su ka kara farashi sun hada da kayan sawa takalma gas da kudin hayar gidaje da kuma taba sigari.

Ya kara da cewa tashin farashin kayan ya fara ne tun daga lokacin Bukuwan Kirsimeti da sabuwar shekara.

Ya ce tun kafin kayayyakin su kara kudi sai da aka kwashe tsawon wata takwas farashin kayayyaki na sauka a Najeriya.

Shugaban ya ce Jihar Ebonyi itace kan gaba wajen yawan tashin farashin kayayyaki inda kuma Jihar Kwara ta fi ta samu raguwar kayayyaki.

Jihar Kogi kuwa tafi samun matsalar tsadar kayan abinci inda ita kuma Jihar Edo ta fi samun saukin kayan abinci a watan Disamban da ya gabata a Najeriya

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: