Gwamnan Jihar Zamfara ya bayyana cewa ayyukan ‘yan bindiga ba zai yanke ba sakamakon samun wasu mutane da su ke tallafa wa yan bindiga.
Gwamnan ya bayyana hakan bayan gama tattaunawar da su ka yi da shugaban kasa a fadar sa da ke Abuja a ranar Litinin.
Ya kara da cewa a na cigaba da samun nasara a harkar tsaron Najeriya duk da wasu su na da hannu a cikin ayyukan ‘yan bindiga.
Ya ce shugaban kasa ya na kokari matuka wajen ganin an magance matsalar tsaron a kasa.
Gwamna Bello Matawalle ya karya ta jita jitar cewa ‘yan bindiga sun kashe mutane 200 a garuruwan Bakuyum da Anka na Jihar,Inda ya ce mutane ne 58 su ka rasa rayukan su.
Gwamnan ya ce gwamnatin sa za ta cigaba da zurfafa bincike don ganin an gano wadanda su ke da hannu a ciki ayyukan ‘yan bindiga domin daukar mataki a kan su.