Majalisar zartarwa a Najeriya ta ce ta za ta fara tuntubar masu ruwa da tsaki a ɓangaren man fetur domin tattauna wa don cimma matsaya a kan ƙarin farashin man fetur din da za a yi ba da jima wa ba.

Minsitan yaɗa labarai a Najeriya Lai Mohammed ne ya sanar da haka jim kaɗa bayan zaman majalisar da su ka yi a Abuja ranar Laraba.
Ya ce za a fara tuntuɓar ma’aikatun da su ke da alaƙa da ɓangaren domin kafin yanke hukunci na ƙarshe.

Zaman majalisar da aka yi ranar Laraba wanda mataimakin shugaban ƙasa Farfesa Yemi Osinbajo ya jagoranta an tattauna a kan batun ƙarin man fetur da ake shirin yi a watan Farbarairu mai kama wa.

Rahotanni na nuni da cewar majalisar na duba yiyuwar mayar da litan man fetur zuwa naira 302 maimakon 162 zuwa 165 da ake siyar da shi a halin yanzu.
Amincewar hakan ya biyo bayan zaman da kwamitin majalisar ya yi da kamfanin mai a Najeriya NNPC.
A zaman majalisar na jiya a amince da wasu ayyuka da ake tsara za a yi a babban birnin tarayya Abuja.