Daga Amina Tahir Muhammad

An samu rudani lokacin da jami’an tsaro suka yi musayar wuta a lokacin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ke kaddamar da gadar Kawo da ke tsakiyar birnin Kaduna, a yau Alhamis.
Yanzu haka Buhari yana Kaduna domin kaddamar da ayyukan da Gwamna Nasir El-Rufai ya aiwatar a Kafanchan, da cikin Kaduna da kuma Zariya.

Sai dai an samu hatsaniya tsakanin jami’an tsaron da ke da alaka da shugaban kasar da kuma wadanda ke Kaduna, inda aka yi ta musayar wuta.

Rikicin dai ya fara ne lokacin da wasu jami’an hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) suka tare hanyar zuwa gadar Kawo jim kadan bayan shugaban da ya hau gadar.
Gwamna Nasir El-Rufai, wanda tun farko ya sauka daga motarsa, ya bi ayarin shugaban kasar zuwa gadar.
Jami’an tsaron da suka hana ‘yan jarida da sauran manyan baki shiga gadar Kawo, sun tare hanyar ne bayan El-Rufai da shugaban kasa suna kan gadar.
Sai dai kuma, mai taimakawa El-Rufai-De-Camp (ADC) ya dage cewa dole ne a bar motar gwamnan ta shiga.
Daily Trust ta ruwaito cewa, hadiman shugaban kasa kan harkokin tsaro sun tsaya tsayin daka kuma hakan ya haifar da ba kawai cece-kuce ba amma an yi ta musayar wuta.
Daga karshe dai an baiwa motar gwamnan damar shiga.