Wata babbar kotu a jihar Bauchi ta yanke wa wasu matasa uku hukuncin zama a gidan kurkuku na tsawon shekaru 17 ba tare da zaɓin tara ba.

Alƙalin kotun Justice Mu’azu Abubakar ne ya karanto hukuncin bayan da aka samu matasan uku da aikata fashi da makami wanda su ka ƙwaci naira dubu sittin.
Matasan da su ka haɗa da Mu’azu Ya’u, Adamu Abdullahi, da Auwalu Babayo an gurfanar da su a gaban kotun a shekarar 2018.

Laifin da kotu ta samu matasan sun aikata ya ci karo da sashe na 97 na kundin dokokin jihar Bauchi wanda aka samar a shekarar 2006.

Matasan sun yi amfani da addina da sandina yayin da su ka yi wa wani mai suna Abdullahi Ahmadu fashin kudin sa naira dubu sittin.
Alƙalin kotun Mu’azu Abubakar ya bayar da umarnin aike da matasan gidan gyaran hali har tsawon shekaru 17 ba tare da zaɓin tara ba.