Hukumar hana cunkuson ababen hawa a jihar Kano KAROTA ta rage harajin da ta saka wa masu tuƙa babur mai ƙafa uku da aka fi sani da adaidaita sahu.
Hakan ya biyo bayan zaman sulhu da aka yi tsakanin hukumar da wakilan ɓangaren masu tuka babur mai ƙafa uku.
Hukumar ta rage adadin harajin da masu tuƙa babur ɗin za su dinga biya a duk shekara daga naira dubu takwas zuwa naira dubu biyar, yayin da aka mayar da sabuwar rijistar naira dubu goma sha biyu maimakon naira dubu goma sha takwas da hukumar ta saka a baya.
Matuka babur mai ƙafa uku wato Adaidaita sahu sun tafi yajin aiki na tsawon kwanaki biyu a makon da ya gabata, domin nuna rashin amincewa a bisa tsarin harajin da su ka ce ya yi musu yawa.
Tsaikon da aka samu na tafiya yajin aikin da su ka yi a makon da ya gabata ya jefa al’ummar jihar cikin mawuyacin halin kasancewar ƙarancin ababen hawa na haya wanda hakan ya sa masu babura da masu motocin da ba na haya ba daukar fasinja domin rage musu radadin rashin abin hawa.
Daga bisani sun koma aikin su bayan da aka cimma matsaya tare da samar da yarjejeniya daga gwamnati na amincewa da rage kuɗin da za a dinga karɓa daga hannunsu.
Daga cikin ƙarin matsayar da aka cimma akwai samar da ƙarin wurin tsayawar masu Adaidaita sahu, sannan za a biya harajin ne a rarrabe, kamar dubu biyu, ko dubu uku ga masu hali su biya nairaa dubu biyar.
Haka zalika an kara wa’adin biyan kudin zuwa ƙarshen watan Fabrairu sannan za a tabbatar an kare mutuncin matuka baburin tare da hukunta duk wani jami’in Karota da aka smau da cin zarafin guda a ciki.
Sai kuma bayar da dama domin ƙirƙirar sabuwar ƙungiya wadda su ka aminta da ita.