Shugaban ƙungiyar Kayode Fayemi ne ya sanar da haka bayan wani zama da ƙungiyar ta yi da mambobinta a kan batun ƙara farashin man fetur.

Shugaban ya ce duba ga yunƙurin da gwamnati ke yi na ƙara farashin man fetur zuwa naira 302 za su zauna da ƙungiyar ƙadago domin lalubo hanyar da za a fahimtar da ƴan ƙasar yadda za a sauka daga tunanin zanga-zanga.
Ya ƙara da cewa ƙuniyar gwamnonin za ta zana da ƙungiyoyin NLC da TUC domin ganin an shawo kan batun fita zanga-zanga da aka tsara.

Sannan ya ce za su duba hanyoyin da za a bi domin ganin ba a samu ƙarin farashin kayyaki ba bayan ƙara farashin man fetur.

Tun tuni ƙungiyar gwamnonin ke kira ga gwamnatin tarayyar Najeriya domin ganin an janye tallafin man fetur baki ɗaya. Bayan zaman da majalisar zartarwa ta yi ta fara nazari a kan mayar da litar man naira 302 maimakon 162 zuwa 165 da ake siyar da shi a halin yanzu.