Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tabbatar wa mazauna garin Kaduna kudirin gwamnatin sa na murkushe yan ta’adda da masu aikata miyagun laifuka a jihar da sauran sassan kasar nan.

Buhari ya yi wannan jawabin ne da yammacin juma’a a Kaduna a wajen taron liyafar da Gwamna Nasir EL Rufa’I ya shirya yayin da shugaban ya bude wasu ayyuka a jihar.
Shugaba Buhari wanda ya yaba da goyon bayan da jihar ke baiwa jami’an tsaro ciki har da kafa ma’aikatar da aka sadaukar domin tsaron cikin gida.

Buhari ya bayar da tabbacin ci gaba da aikin murƙushe yan ta’adda domin samar da ƙarin ci gaba a jihar da ma ƙasa baki ɗaya

Sannan ya bayyana jin dadin sa a bisa damar buɗe ayyuka da aka bashi a jihar wanda ya yaba wa gwamnatin jihar a bisa kokarinta.
A nasa jawabin gwamna El Rufa’I yayi kira da a kara ƙarfafar ayyukan soji domin dalike ayyukan yan ta’adda a jihar.