Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya ce gwamnatin sa za ta tabbatar an gaggauta yanke hukuncin kisa a kan wanda ake zargi da kashe ɗalibar sa a jihar.

Gwamna Ganduje ya bayyana haka ne yayin da ya je ziyarar ta’aziyya gidan su Hanifa Abubakar bayan da aka tabbatar da rasuwarta.

A cikin wata sanarwa da babban sakataren yaɗa labaran gwamnan Kano Malam Abba Anwar ya sanyawa hannu gwamnan ya ce ya na da tabbacin za a gudanar da shari’ar kuma a kammala ta tare da tabbatar da cewar an zartar da hukuncin da kotu ta yanke.

Sannan gwamnatin za ta bai wa iyayen ɗalibar da aka hallaka kulawar da ya kamata.

A bisa batun makarantu masu zaman kansu kuwa, gwamnatin Kano ta ce za ta duba matakin da za ta ɗauka don hana afkuwar hakan a nan gaba.

Gwamna Ganduje ya kai ziyarar ta’aziyyar ne a yau Litinin tare da rakiyar mataimakinsa da shugaban masu rinjaye a majalisar dokokin jihar Kano da wasu muƙarraban gwamnatin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: