Hukumar kwadago a Najeriya reshen jihar Kano ta bayyana matsayar gwamnatin tarayya na soke yunkurin janye tallfin man fetr a matsayin gagarumar nasara.

Shugaban kungiyar Kabiru Ado Minjibir ne ya sanar da hakan a ya Talata.

Ya ce matsayar da aka cimma na janye kudirin gwamnatin tarayya nasara ce ga dukkanin yan kasar.

Kungiyar kwadago ta shirya shiga zanga-zanga a watan da mu ke ciki domin nuna rashin goyon bayanta a kan yunkurin janye tallafin man fetur da gwamnatin ke shirin yi a baya.

Gwamnatin tarayya ta anye kudirin nata ne bayyan da ta gaza samun goyon bayan yan kasar wadanda ke kallon hakan a matsayin hanyar da za a kara samun yawan matalauta a Nageriya.

A baya gwamnatin ta yi yunkurin mayar da man fetur naira 302 maiimakon 162 zwa 165 da ake siyar da shi a halin yanzu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: