Daga Amina Tahir Muhammad

Hukumar zabe mai zaman kanta ta ƙasa ta ce tayi wa sabbin mutane 5,173,335 rijistar katin zaɓe a karo na uku na ci gaba da rijistar kuri’a a fadin kasar.
INEC ta bayyana haka ne a wani sabon rahotonta na mako-mako kan rijistar katin zaɓe.

Hukumar ta bayyana haka ne a Abuja a ranar Litinin, ta kuma bayyana cewa masu rajista 2,665,421 sun kammala rajista ta yanar gizo da kuma ɗaukar hotunan su.

Bisa ga kididdigar da aka sabunta ta ƙunshi maza 1,344,813, da mata 1,320,608.
Alkaluman sun nuna cewa mutane 24,723 daga cikin alkaluman mutane ne masu fama da nakasa yayin da 1,854,371 matasa ne tsakanin shekaru 18 zuwa 34.
An kuma lura cewa daga cikin mutane 2,665,421 da suka kammala rajistar su, 1,092,742 sun yi rajista ta yanar gizo, yayin da 1,572,679 suka yi rajistar ta ƙafa da ƙafa.