Gwamnatin Jihar Kwara ta umarci dukkan mata musulmi na Jihar da su dinga sanya hijabi idan za su je makarantun gwamnati.

Umarnin hakan na zuwa ne tun bayan da aka samu rikicin addani a jihar a kan haramta sanya hijbi a makarantun.
Gwamnatin ta umarci makarantun na gwamnati da su sanya dokar a dukkan fadin makarantun Jihar.

Gwamnatin Jihar ta Kwara ta bayyana cewa ‘yan mata musulmi wadanda za su shiga makarantar gwamnati su na da ‘yanci da za su saka hijabi a makarantun gwamnati.

Kwamishiniyar ilmin Jihar ita ce ta sanar da hakan a taron zaman lafiya da ya gudana da masu ruwa da tsaki na musulmai da kiristoci a Jihar.
Kwamishiniyar ta bukaci shugabannin Musulmin jihar da kiristoci da su bada hadin kai wajen ganin Jihar ta zauna Lafiya.
Sannan ta yi gargadi ga dukkan mai shirin kawo cikas ga zaman lafiyar a cikin al’ummar Jihar zai fuskanci hukunci mai tsanani.
Taron ya samu hallartar manyan baki daga bangarori da dama na Jihar ciki har da shugabannin addinin musulinci da na kiristoci