Wani matashi mai shekara 25 mai suna Naziru Badamasi ya kashe kansa ta hanyar rataya a garin Tsadawa cikin karamar hukumar Taura ta Jihar.

Kakakin ‘yan sandan Jihar ASP Lawan shisu shi ne ya tabbatar da faruwar Lamarin a yau Talata.

Ya ce an samu mutumin ya rataye kan sa a jikin Bishiya a kauyen zangon Maje da ke karamar hukumar hukumar Tauura ta Jihar.
Sannan ya yi amfani da wandon sa waje rataye kan na sa a ranar Litinin.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Jihar ya bayyana cewa sun samu kira ne daga hakimin garin wanda ya shaida musu lamarin da ya faru.

Ya ce wanda ya kashe kan nasa ya na da tabin hankali kuma yabar gida da misalin karfe goma sha biyun rana inda ya tai ya kashe kansa.

ASP Lawan shisu ya ce tun bayan samun Labarin su ka aike da jam’an su wajen da lamarin ya faru tare kuma sun dakko gawar wanda ya rataye kan sa sannan su ka mika shi asibiti kuma likitoci su ka tabbatar da mutuwar sa.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: