Ƙungiyar malaman firamare sun shiga yajin aiki bayan gaza biyansu wasu haƙƙoƙinsu da aka ƙi yi.

Shugaban ƙungiyar reshen Kubwa ya shaida wa Daily Trust cewar rashin biyansu haƙƙoƙinsu ne ya sa su ka tsunduma yajin aikin.

Kwamared Ameh Baba ya ce daga cikin dalilan da ya sa su ka shiga yajin aikin akwai rashin ƙarin girma ga malaman da su ka camncanta waɗanda aka ƙi yi musu tun daga shekarar 2011.

A watan Disamban shekarar da ta gabata, an cimma matsaya bayan shiga tsakanin ƙungiyar da ɓangaren gwamnati, alƙawarin da aka gaza cikawa.

A shekarar da ta gabata ƙungiyar ta tafi yajin aikin sau uku kuma har yanzu ba a kai ga cimma matsaya tare da cika alƙawuran da aka ɗaukar musu ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: