Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya soke ziyarar da ya shirya kai wa jihar Zamfara a yau bayan samun sauyin yanayi.
Gwamnan jihar Muhammad Bello Matawalle ne ya sanar da haka a yau bayan da shugaban ya ɗage ziyarar da ya shirya kai wa domin jajanta wa mutanen da hare-haren ƴan bindiga ya rutsa da su.
Gwamnan ya ce shugaban ya sanar da shi ɗage ziyarar tare da neman afuwar jama’ar jihar a bisa rashin halartarsa Zamfara a yau.
Shugaba Buhari ya ziyarci jihar Sokoto a yau domin ƙaddamar da kamfanin samar da siminti na BUA.
Shugaban ya ɗage ziyarar, kuma kafin haka ya shiya zuw jihar Zamfara a yau wanda aka tsara ai gana da shugabannin gargajiya da jami’an staron jihar da kuma mutanen da hare-haren ƴan bindiga ya shafa.
Shugaba Buhari ya nemi afuwar ƴan jihar a bisa rashin halartar sa ziyarar da aka tsara zai je a yau Alhamis.