Daga Amina Tahir Muhammad

Shugaban kasa Muhammadu Buhari  ya umarci sojoji da sauran jami’an tsaro da su tunkari duk wani mutum ko kungiyar da ke kawo cikas ga kokarin samar da zaman lafiya da tsaro da kwanciyar hankali a kasar.

A cewar mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai Femi Adesina, ya ce Buhari ya bayyana haka ne a lokacin da ya kai ziyara fadar mai alfarma Sarkin Musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar III a yau Alhamis.

Buhari Ya ce “Na ba su cikakken umarni da kada su bar duk wani dan fashi ko ‘yan ta’adda da ke barazana ga rayuka da dukiyoyin ‘yan Najeriya da ba su ji ba ba su gani ba.”

A cewar Adesina, Buhari ya jajanta wa gwamnati da al’ummar Sakkwato kan hasarar rayuka da dukiyoyi da aka yi a baya-bayan nan sakamakon munanan hare-haren da ‘yan bindiga da wasu gungun miyagu ke kaiwa.

Ya ce shugaban ya tabbatar wa jama’a cewa zai ci gaba da jajircewa wajen ganin an kawo karshen munanan ayyukan ta’addanci a jihar da sauran sassan kasar nan.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: