Daga Khadija Ahmad Tahir

Kungiyar kiritoci ta CAN treshen jihar Kwara barranta kanta daga goyon bayan saka hijabi ga ƴan makaranta.

Ƙungiyar ta  musanta hakan ne a wata wasika da ta fitar ta hannu shugabannin kungiyar waɗanda su ka bayyana wa manema labarai ranar Alhamis.

Shugabannin kungiyar sun gargadi gwamnatin jihar da ka da ta tilastawa daliban makarantun na kiristoci saka hijabi domin gujewa tashin hankali a Jihar.

Kungiyar ta kara gargaɗin gwamnatin jihar a kan kada ta tsaurara domin gujewa tashin hankali a jihar.

Kungiyar ta CAN da sauran makarantun jihar sun bayyana cewa babu dalibar da za ta zauna a cikin aji idan ta sanya hijabi.

CAN ta gargadi gwamnati da kada ta matsantawa daliban jihar sanya hijibi idan za su makaranta domin gujewa rikicin addinai wanda aka tabayi a baya.

Kungiyar ta ce babu wani taron da su ka yi da ma’aikatar ilmin Jihar kamar yadda gwamnatin Jihar ta bayyana a ranar 24 ga watan Janairun 2022 cewa ta yi taro da kungiyar kiristocin inda kungiyar ta musanta hakan.

Gwamnatin Kwara ta bayar da damar saka hijabi ga ɗalibai mata a makarantu kamar yadda ta sanar a kwanan nan.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: