Aƙalla mutane biyu ne su ka rasa rayukansu yayin da gidaje sama da 30 su ka ƙone a sakamakon wata gobara da ta tashi a wata motar dakon mai.

Al’amarin hya faru a safiyar yau a yankin Ohoro da ke ƙaramar hukumar Ughelli North ta jihar Delta.

Rahotanni sun nuna cewar wasu motoci sun ƙone yayin da aka yi asarar dukiya mai tarin yawa.

Wasu shaidun gani da ido sun tabbatar da cewar wutar ta fara ne daga jikin wata babbar motar dakon mai lamarin da ya shfi sauran gidaje da ababen hawa.

Mun yi koƙarin ji daga hukumar kashe gobara ta jihar Delta sai dai har lokacin da mu ke kammala rahoton ba mu ji daga gare su ba.

Wasu mazauna yankin sun shaida cewar, motar dakon ta ɗakko man fetur ne lamarin da ya sa gobarar ta ƙazanta.

A mafi yawan lokutan sanyi a kan samu yawaitar tashin gobara wanda hakan kan yi silar rasa rayuka da dukiya mai yawa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: