Daga Khadija Ahmad Tahir

Sarkin Katsina Alhaji Abdulmumin Kabir Usman ya bayyana hakan ne a fadar sa a lokacin da mataimakin shuguban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya kai masa ziyara tare da ta aziyar mahaifiyar Alhaji Dahiru Mangal a ranar Lahadi.

Sarkin ya nuna damuwar sa game da hare-hare da ‘yan bindiga su ke kai wa a Jihar.

Sarkin ya ce wannan shi ne karon farko da mataimakin shugaban ƙasar ya je jihar tun bayan da aka yi yakin neman zabe a Najeriya inda ya zuwan Osinbajo gare su yana cike da dumbum tarihi.

Ya kara da cewa shi da gwaman Jihar sam ba sa iya bacci sakamakon rashin tsaro da ya addabi Jihar, kuma ya ji dadin da aka bayyana ‘yan bindiga a matsayin ‘yan ta adda.

A nasa bangare mataimakin shugaban kasar ya bayyana jin dadin sa sakamakon ci gaban da aka samu a ɓangaren staron jihar.

Osinbajo ya bayyana cewa shugaban kasa muhammad Buhari ya gana da shugabannin da ke kula da harkar tsaro domin shawo kan tabarbarewar tsaro da ta addabi Najeriya baki daya tare da samar da sauye sauye akan sa.

Mataimakin ya ce dukkanin tsare-tsare da sauye sauye da gwamnatin tarayya ta saka za su fara aiki nan bada dadewa ba a kasa baki daya.

Tun da fari farfesa Yemi Osinbajo ya fara kai ziyara gidan Alhaji Dahiru Mangal daga bisani ya wuce fadar Sarkin Jihar Katsina a ranar Lahadi.

 

 

 

 

 

 

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: