Hukumar kashe gobara a jihar Kano ta tabbatar da mutuwar wasu mutane biyu a sanadiyyar kifewar wani kwale-kwale a ƙaramar hukumar Rimin Gado a jiharr.

Mai magana da yawun hukumar Saminu Yusif ne ya bayyana hakan ya ce lamarin ya faru a safiyar yau Litinin.

Saminu Yusif ya ce mutanen sun hau kwale-kwalen ne daga ƙauyen Zangon Durgu zuwa ƙauyen Kanya duka a ƙaramar hukumar Rimin Gado.

Yayin da su ka isa wajen bayan karɓar kiran waya daga wani Barista Munir Dahiru sun tarar da mutane biyu a raye yayin da sauran biyun aka tabbatar sun rasa rayukansu.

Tuni su ka miƙa gawar mamatan ga mataimakin shugaban ƙaramar hukumar Rimin Gado.

Saminu Yusif ya ce mutane biyun da su ka rasa rayukansu baki ɗaya sun haura sama da shekara 30 a duniya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: