Wasu da ake zargi ƴan bindiga ne sun abka wasu ƙauyuka a garin Daddarar da ke ƙaramar ukumar Jibia kuma su ka kashe mutane shida ciki har da wani mai unguwa

Al’amarin ya faru a daren jiya Laraba yayin da su ka yi wa ƙauyukan ƙawanya.

Wani mazaunin garin ya tabbatar da cewar bayan mutanen da aka kashe akwai wasu da dama da su ka samu rauni.

Ya ƙara da cewa ƴan bindigan sun karɓi kuɗaɗe daga mazauna garin sannan su ka kwashe kayan amfani da dabbobin su.

Haka kuma akwai wasu mutane da ƴan bindigan su ka yi awon gaba da su a yayin da su ka kai harin.

Yayin da ya ke tabbatar da hakan ga manema labarai, kakakin ƴan sandan jihar SP Gambo Isah ya ce mutane biyar aka kashe daga ciki har da wani mai unguwa.

Ya ƙara da cewar na cikon shidan ba a san inda yake ba ballae a tabatar ya na raye ko ya mutu.

Ya ce jami’ansu hadin gwiwa da sauran jami’an tsaro sun yi ƙoƙarin daƙile harin, ama duk da haka akwia wata mace guda da ba a ganta ba.

Gambo sa ya ce akwai wasu da ake zargin ƴan bindiga da su ke guduwa daga jihohin Zamfara da Sokoto su na samun mafaka a Katsina, sai dai su na ƙoƙarin ganin hakan ba ta kasance ba.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: