Hukumar lafiya ta duniya WHO ta ce cutar sankara wadda aka fi sani da kansa na hallaka mutane dubu ɗari bakwai 700,000 a kowacce shekara.
Daraktan hukumar na shiyyar Afrika Dr. Matshido Moeti ne ya sanar da haka a yayin da ake bikin ranar masu cutar kansa.
Daraktan ya ce ya na samun masu ɗauke da cutar miliyan goma sha ɗaya 11,000,000 a kowacce shekara.
Ya ce ana samun rahoton yaduwar cutar wanda ya ƙunshi kansar mama, kansar jini da kuma kansar mafitsara.
Daraktan ya yi kira ga sauran mahukunta a hukumar musamman shiyyar Afrika da su ƙara ƙaimi a kan ayyukansu ganin yadda cutar ke ƙara bazuwa tare da yin ta’adi a cikin al’umma.
Ya ƙara da cewa a bisa alamu da yadda cutar ke hallaka mutane akwai barazana a nan gaba wanda ake zargin ta’adin zai zarce tunanin da ake yi a yanzu.