Sabon shirin nan na bunkasa noma wanda da kiwo na Jihar Kano KSADP shirin da gwamnatin Jihar Kano karkashin Mai Girma Gwamna Dr. Abdullahi Umar Ganduje ta kirkiro kuma ya samu tallafin kudi daga bankin addinin musulunci dake Jidda da wasu hukumomi wanda hukumar bunkasa aikin gona ta KNARDA ta ware wani bangare domin lura da shirin yana samun bunkasa.

A daidai lokacin da shirin ya shiga shekarar sa ta biyu cibiyar Sassakawa Africa Association (SAA) tayi taron masu ruwa da tsaki a shirin da suke hada da ICRASAT, IITA kamfanunuwan saye da sayarwar kayan amfanin gona da bunkuna.
Domin jin rahotannin irin abubuwan da suke gaba a shirin. Taron ya samu halartar Mataimakin Gwamnan Jihar Kano Dr. Nasiru Yusuf Gawuna wanda shine shugaban kwamitin, Gawuna ya samu wakilcin babban sakatare a ma’aikatar gona ta Jihar Alhaji Balarabe Karaye inda ya nuna jin dadi da gamsuwar sa akan yadda shirin yake gudana tunda fari.

Shugaban Sassakawa na kasa Prof. Sani Miko yayi tsokaci akan yadda cibiyar tasa ta himmatu wajen ganin ta sauke nauyin da ake dora mata.

Shi ma shugaban hukumar KNARDA Dr. Junaidu Yakubu Muhammad da shugaban gudanar da shirin na jiha Mal. Ibrahim Garba sun yaba tare da tabbatar da gaskiya da Sassakawa ke yi wajen aiwatar da shirin na KSADP.
Sannan mahalarta taro musamman masu ruwa da tsaki sun tattauna inda a ƙarshe aka gamsu anyi nasara kuma za’a ribanya nasarar anan gaba.
Daga bisani aka raba babura guda (29) ga malaman gonar da ake wannan aiki dasu ƙari akan guda (90) da aka raba a shekarar data gabata inda shugaban shirin na Jiha Mal. Ibrahim Garba yayi albishirin sahalewar cibiyar ta Sassakawa siyen guda (100) nan gaba duba da irin kokarin da sukayi na siyan ingatattun babura.
Suma wadanda suka rabauta da wadannan babura sun nuna jin dadin su, tare da aniyar rubanya kokarinsu wajen gudanar da ayyukan dake gabansu.