Daga Khadija Ahmad Tahir
Hukumar Hisbah a Kano ta kama wasu kwalaben barasa guda 3,800,000 tare da fasa su.
Kwamandan Hukumar Hisbah a Kano Ustaz Haruna Ibn Sina shi ne ya bayyana kwace kwalaben tare kuma da fasa su a unguwar Tudun Kwalebawa da ke karamar hukumar dawakin Tofa a ranar Laraba.
Kwamandan ya kuma kara da cewa hukumar ta na cigaba da samun nasara wajen yaki da masu shan kayan maye tare da dakile miyagun halaye a cikin jama’a.
Gwamnan Jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana jindadin sa bisa jajircewar da hukumar ta Hisbah ke yi wajen yaki da miyagun dabi u a jihar Kano.
Dan majalisa mai wakillar Albasu Sunusi Usman Batayya shi ne wanda ya wakilci gwamna ganduje a lokacin da aka fasa kwalaben giyar.
Hukumar Hisbah ta sha alwashin cigaba da yaƙi da munanan ɗabi’u a lungu da saƙo najihar Kano baki ɗaya.