Kamfanin mai a Najeriya NNPC ya bayar da umarnin kaddamar da bincike tare da dakatar da wasu kamfanoni da ake zargin sun shigo da urɓataccen man fetur.

Shugaban kamfanin Mele Kyari ne ya bayyana sunayen kamfanonin da ake zargi bayan jama’ar ƙasar sun koka ganin yadda gurɓataccen man ya lalata ababen hawa da dama.

Kamfanonin da ake zargi sun haɗa da MRS, Oando da Duke Oil sai kamfanin Emadeb.

NNPC ya ce ya samu rahoton shigo da gurɓataccen man tun a ranar 20 ga watan Janairun shekarar da mu ke ciki.

Ya ce tun a watan Janairun mutane ke ƙorafi tare da kokawa a kan gurɓataccen man fetur ɗin da aka shigo da shi wanda ya lalata ababen hawa masu yawa.

A halin da ake ciki kamfanin ya rufe kamfanonin da aka samu sun shigo da gurɓataccen man tare da fara binciken musabbabin hakan.

Leave a Reply

%d bloggers like this: