Rahotanni na nuni da cewar wasu ƴan bindiga sun kashe wani jami’in ɗan sanda tare da wasu jami’an hukumar kwastam a jihar Enugu.

Al’amarin ya faru a yau da misalin ƙarfe ɗaya da rabi na rana.
Ƴan bindigan sun kai hari wani shingen bincike na jami’an kwastam da ke kan babbar hanyar Enugu zuwa Fatakwal.

Wani da al’amarin ya faru a kan idonsa ya shaida cewar, an hallaka wasu jami’an tare da jikkata uku daga ciki.

A sanadiyyar hakan matafiya da dama sun samu jinkiri ganin yadda lamarin ya kasance.
Jami’in hulɗa da jama’a na ƴan sanda a jihar ASP Daniel Ndukwe ya tabbatar da lamarin sai dai ya ce su na kan tattara bayanai kafin bayyana ainahin abin da ya faru.