Ƴan majalisar dokokin jihar 18 ne su ka rataɓa hannu domin nuna goyon bayan tsige mataimakin gwamnan jihar Barista Mahdi Aliyu Muhammad.

Hakan ya faru a jiya Alhamis yayin zaman majalisar.
Babban daraktan yaɗa labarai a majalisar Mustapha Jafaru Ƙaura ne ya sanar da hakan bayan wasu daga cikin ƴan majalisar su ka kai ƙudirin hakan zauren majalisar.

Jim kaɗan bayan gabatar da ƙudirin wakilai a zauren majalisar su 18su ka rattaɓa hannu domin nuna goyon bayan su.

Matakin tsige mataimakin gwamnan ya biyo bayan wani zargi da ake yi a kansa ake so a gudanar da binike tare da ɗaukar matakin da ya dace.