Daga Amina Tahir Muhammad

Gwamnan jihar Borno, Babagana Uamara Zulum, ya ce jagorancin shugaban kasa Muhammadu Buhari tare da na jam’iyyar APC shi ne zai tabbatar da nasarar jam’iyyar a zaben 2023 mai zuwa.

Zulum ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a a lokacin da ya karbi baƙoncin ƙungiyar Progressive Consolidation Group da ke goyon bayan mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo a zaben shugaban kasa na 2023.

A ziyarar da ƙungiyar Pro-Osinbajo ta ziyarci Zulum domin neman goyon baya’, gwamnan ya shaida wa kungiyar cewa za ta iya shafar jam’iyyar muddin ‘yan kungiyar ba su bi umarnin shugaba Buhari da APC ba a zaben.

Zulum ya ce gabanin zaben 2023 abin da ya fi dacewa da masu ruwa da tsaki shi ne  hadin kan jam’iyyar domin samun nasararta

Sannan ya buƙaci ɗaukacin shugabanin da su yi ƙoƙarin ganin an samu haɗin kan jam’iyyar da kuma zaman lafiyar kasa. Zulum ya ce ya zama wajibi a bi tsarin shugabancin shugaban kasa gabanin zaben 2023.

Bugu da kari, ya bayar da tabbacin cewa jihar Borno ta na maraba da magoya bayan dukkan shugabannin jam’iyyar APC masu kishin kasa, tare da bayyana cewa jam’iyyar dunƙulalliya ce.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: