A yau kotu za ta fara sauraron ƙarar da ake zargin wani Abdulmali Tanko da hallaka ɗalibarsa Hanifa Abubakar mai shekaru biyar a duniya.

Babbar kotun jihar Kano ce za ta fara sauraron ƙarar bayan da gwamnatin Kano ta gurfanar da mutane uku da ake zargi a gaban ta.

Ana zargin Abdulmalik Tanko da matarsa da kuma wani abokinsa a zargin hada kai tare da garkuwa da wata ɗaliba mai shekaru biyar.

Bayan yin garkuwa da ita sun buƙaci a basu kudin fansa naira miliyan shida daga bisani kuma su ka kashe ta.

Bayan gurfanar da su a gaban kotu tun a farko, kotun ba ta saurari ƙarar ba saboda babu lauyan da ke tsayawa mutane ukun da ake zargi.

Kotun ta buƙaci gwamnatin Kano ta su lauyan da zai tsayawa waɗanda ake zargi wanda lauyan gwamnatin Kano ya tabbatar da cewar za a cika wannan umarni.

Babbar kotun jihar Kano za ta fara sauraron karar a yau da misalin ƙarfe biyu na rana.

Leave a Reply

%d bloggers like this: