Ƙungiyar malaman jami’a a Najeriya sun fara yajin aikin gargaɗi na wata guda tun bayan gaza cimma matsaya da kuma rashin cika alƙawuran da su ka ce gwamnati ta ƙi musu.

Ƙungiyar ta sanar da tafiya yajin aikin bayan da ta shafe sama da mako guda ta na tattauna wa a kan yadda za ta fuskanci yajin aikin da ta shiga a halin yanzu.

Hukumar zartarwa a ta ƙungiyar ce ta sanar da shiga yajin aikin a yau Litinin wanda shugaban ƙungiyar Frafesa Emmanuel Osodeke ya sanar a Kegas.

Ƙungiyar ta buƙaci malaman jami’a su yi biyayya da umarninta na tafiya yajin aikin wanda su ke kallon hakan a matsayin hanyar za ta sanya gwamnatin ta waiwayi buƙatunsu.

Wasu daga cikin dalilan da ya sa ƙungiyar ta tafi yajin aikin su ne rashin biyansu albashinsu da alawu-alawus, da kuma rashin ƙarin girma ga waɗanda su ka cancanta sai kuma wasu gyare-gyare da kula da walwalar malaman.

A shekarar 2022 da mu ke ciki, wannan ne karo na farko da ƙungiyar ta fara yajin aikin duik da cewar ta sha tafiya yajin aikin a baya amma aka gaza cika musu burinsu.

Gwamnatin Najeriya ta sha zama da ƙungiyar domin yin sulhu amma har wa’adin da aka ɗauka ya cika ba a kai ƙarshen matsalar da ƙungiyar ke kokawa da gwamnati a kai ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: