Hukumar kula da ingancin abinci ta ƙasa a Najeriya NAFDAC reshen jihar Kaduna ta ce ta kama maganin ƙarfin maza mai yawa a jihar.

Shugaban hukumar Nasiru Mato ne ya sanar da haka a ranar Litinin yayind  aya ke gana wa da manema labarai.

Ya ce an kama magungunan ne domin ba su da shaidar izinin siyarwa daga hukumar.

Ya ƙara da cewa hukumar na ƙoƙarin ganin ta wayar da kan mutane a kan illar amfani da nau’in magungungan da kuma illar da ya ke haifarwa ga lafiyar jikin mutane.

Daga cikin magungunan da hukumar da kama akwai Power Cofee, Honeymoon, Viga 150000, Zahidi Coffee, da kuma Big Boss.

Hukumar ta ce magungunan na illata lafiyar jiki a wasu lokutan ma ta na silar rasa rayukan mutane da dama.

Shugaban ya shawarci mutane da su dinga amfani da magungunan da likitoci su ka ɗora su a kai domin samun kuzari wajen jima’i.

Leave a Reply

%d bloggers like this: