Ƙungiyar ɗalibai a Najeriya ta yi barazanar shirya zanga-zanga a kan tafiya yajin aikin malaman jami’a.

Shugaban ƙungiyar na ƙasa Sunday Adebayo ne ya sanar da haka a wata sanarwa da ya fitar.

Aanarwar ta nuna damuwa a dangane da yain aikin malaman Wanda ɗaliban su ka ce sam bai musu daɗi ba.

Ƙungiyar ta zargi gwamnatin tarayya da kungiyar malaman jami’a ASUU kan tafiya yajin aikin wanda su ka ce sun ki mayar da hankali don kawo karshen yajin aikin da su ke tafiya.

Ƙungiyar ɗaliban ta ce za ta yanke hukunci tare da zartar da shi a ranar 17 ga watan Fabrairun da mu ke ciki.

Ƙungiyar malaman jami’a ta tafi yajin aiki ne domin nuna fushi bisa gaza cika alkawuran da su ka ce gwamnatin kasar ta ki ɗauka.

Leave a Reply

%d bloggers like this: