Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya aikewa majalisar dokokin Najeriya wasika domin neman amincewa da kafa wata hukuma da za ta lura da wasu daga cikin jami’an tsaron kasar.
Shugaba Buhari ya ce za a samar da hukumar ne domin lura da hukumar kare fararen hula ta Civil Defence da hukumar lura da gidajen gyaran hali da hukumar kashe gobara sai hukumar shige da fice a Najeriya.
Wasiƙar da aka aikewa majalisar mai dauke da kwanan watan 9/02/2022 an karanta ta a zauren majalisar a zamanta na yau Talata.
Bukatar samar da hukumar na karkashin sashe na 58(2) na kundin tsarin mulkin Najeriya wanda aka gyara a shekarar 1999.
Shugaba Buhari ya bukaci majalisar domin yin duba tare da amincewa da bukatar da ya aike mata.