Hukumar Hisbah a Kano ta ce an Samu karuwar bokaye a jihar Kano.

Hukumar ta bayyana haka ne a shafin ta wanda ta ce ta kama akalla bokaye talatin a shekarar da ta gabata.
A cewar hukumar an samu karuwar yawan bokaye a jihar la’akari da yadda aka samu ƙididdigar bokayen a baya.

Hukumar ta ce ta ja hankalin wasu daga cikin bokayen ta hanyar yi musu nasiha kuma daga bisani su ka sake su.

Yayin da wasu daga cikin bokayen aka kai su kotu domin yi musu hukunci.
Haka kuma babban kwamandan hukumar Ustaz Haroon Ibn Sina ya ja hankalin jama’a musamman mata da su kiyaye biyewa bokaye domin gudun sabawa Allah S.W.A.